Dubun wasu miyagun da ke daji a jihar Katsina ta cika, bayan da aka rada ma 'yan sintirin yankin wurin da su ke wani taro da zummar kai wani hari. Bayan arangamar da aka yi dai, Allah ya dora 'yan sintiri kan miyagun, wadanda aka masu yadda su kan yi ma bayin Allah.
Dama 'yan sa Kai da suka harzuka da hare-haren 'yan bindiga a yankinsu, suna sa ido tare da lura da abubuwan dake gudana, wanda hakan ya kai su ga far ma wadan da suke zargin mahara ne, a inda suke tattauna a tsakaninu.
Saboda harzukar da su ka yi da danyen halin miyagun, sun kashe su ta hanyar yankasu, baya ga sauran matakan da akan dauka kan irin wadannan miyagun.
Majiyar Muryara Amurka, wadda ta bukaci sakayawa, ta bayyana cewa saboda tsabar sa ido da kuma lura da kai komon jama'a, gami da hadin kai da jama'a ke bayarwa, ta kai ga samun bayanan sirri cewa wasu da ake zargin mahara 'yan bibdiga ne, suna taro a bayan gari, shi ne 'yan sa kai suka shirya su ka kai masu farmaki tare da aikawa da su lahira.
Ga Sani Shu'aibu Malumfashi da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5