Kimanin kashi 85 daga cikin 100 na al’ummar jihar Kebbi manona ne da Fulani makiyaya. Wanda hakan ke haddasa yawan samun dauki ba dadi tsakaninsu. Manoma da Fulanin suna dorawa junansu laifin wannan yawan tashin hankali da ake samu.
Manoma na zargin shanun da ke fita kiwo na cinye musu amfanin gona, su kuma Fulani na kukan cewa Manoma na bin son zuciya ne wajen cinye iyakokin burtalin shanu da sunan noma, ta inda suka ce shanunsu na rasa hanyar bi idan zasu je kiwo ko lokacin da suke dawowa da maraice.
Hakan ce tasa aka hada wani taron tattaunawa da wayar da kan juna don samun daidaito. Masu bayani daga bangaren Fulanin da na Manoman sun tofa albarkacin bakinsu game da lamarin. Gwamantin jihar Kebbi ma ta ce shirye take don warware matsalar.
Ga rahoton Wakilin Muryar Amurka Murtala Faruk Sanyinna daga Jihar ta Kebbi.
Your browser doesn’t support HTML5