Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ABUJA: Liyafar Matasa Da Matar Shugaba Buhari Na Najeriya


Matar Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari
Matar Shugaban Kasar Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari

Matasa sun taka rawar gani sosai a Najeriya wajen amfani da kafafen sada zumuntar yanar gizo wajen tallata shugaba Muhammadu Buhari don ya zama canjin da zai maye gurbin gwamnatin data gabata, kamar yadda masu tsokaci suka nuna.

Wannan ce tasa wasu ke ganin dalilin da yasa kenan matar Shugaban na Najeriya Aisha Muhammadu Buhari ta hada tare da gayyatar matasan shafukan ire-iren wadannan yanar sada zumuntar don yin liyafa tare da ita.

Matasa da dama daga garuruwa daban-daban na Najeriya ne suka halarci wannan liyafar a birnin Tarayyar kasar wato Abuja. Mahalartan sun hada da garuruwan Kudanci da Arewacin kasar.

Wasu masu gaza gani suna ganin cewa wannan kbarnar kudin kasa ne kawai yasa ta gayyato liyafar. to sai dai wani Malamin Jami'a Dakta Abubakar Umar Kari yana ganin ba wani abin damuwa bane saboda rawar da matasan suka taka.

Ya ma kira matasan da sunan gwarazan al'umma ne ta yanar gizo, sannan matasan suka yi ruwa da tsaki wajen maida kafafen sada zumuncin wajen maida martanin sukar da shi Buharin ya sha lokacin yakin neman karagar mulkin kasar. Ga rahoton Wakiliyarmu Madina Dauda daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG