Cibiyar ‘yan jaridar Nijer ta shirya wani taro ranar Juma’a 10 ga watan Yuli domin nazari akan matsalolin da ke haddasa tarnaki wajen soma zartar da dokar da ta hana a kulle 'dan jarida akan aikinsa, yayin da a yanzu haka jama’ar kasar ke korafi akan wata dokar da gwamnatin kasar ta yi da nufin soma hukunta masu rubuce-rubucen batanci a kafafen sada zumunta.
A shekarar 2010 ne gwamnatin jamhuriyar Nijer ta dauki matakin kare ‘yan jarida daga barazanar zuwa kurkuku saboda dalilai masu nasaba da aikin jarida, sai dai shekaru 10 bayan sa hannu a wannan takarda har yanzu ana fuskantar turjiya ganin yadda ake ci gaba da garkame ‘yan jarida saboda bada labarin da bai yi wa mahukunta dadi ba, dalilin da ya sa cibiyar ‘yan jarida Maison de la Presse ta shirya wani taro domin nazari akan wannan al’amari a cewar sakaren kungiyar mai kula da yada labarai Souleymane Brah.
Wannan na faruwa ne wata daya kacal bayan da majalisar dokokin jamhuriyar Nijer ta ba gwamnatin kasar izinin sauraren hirarrakin jama’a a waya ko yin kutse a kafafen sada zumunta.
Wata alkaliya da ke fafutikar kare hakkin bil’adama Mme Goge Gazibo Maimouna ce aka gayyato domin yi wa mahalarta wannan taro bayani akan abubuwan da wadannan dokoki suka kunsa.
“Mu masanan doka mu muka tsara wadanan dokoki wadanda mafi yawancin lokuta ake dukanku da su ko a bugi ‘yan kasa da su. Dokar hukunta masu batanci a kafafen sada zumunta na daya daga cikin dokoki mafi tsanani a Nijer haka kuma ta na daga cikin dokokin da suka fi sarkakiya. Kwararu ne suka tsara ta to amma yana da kyau a matsayinku na ‘yan jarida ku iya bambanta wadanan dokoki biyu,” a cewar Maimouna.
Halin ko in kula da mafi yawancin ‘yan jarida ke nunawa dokokin da suka shafi aikin jarida a cikin gida na daga cikin manyan dalilan da ke sanadin aika ‘yan jarida gidan yari a Nijer inji editan jaridar la Roue de L’histoire Ibrahim Moussa.
Saurari cikakken rahoton Souley Barma.
Your browser doesn’t support HTML5