Kungiyar ta shirya taron addu'ar ne ganin yadda matsalar tsaro ta addabi kasar kuma abubuwa sai sake tabarbarewa su keyi.
Shugaban kungiyar na kasa Alhaji Aliyu Abubakar yace addu'a ce kadai abun da zasu iya yin anfani da ita domin ganin an kawo karshen kashe kashen da a keyi a kasar wanda yaki ci yaki cinyewa. Yace maimakon kungiyar ta tsaya tana cewa laifin wannan ne ko laifin wancan ne abin da ya fi dacewa shi ne akai kukan 'yan Najeriya zuwa ga Allah wanda yake jin addu'a. Ya kira sauran addinai su ma su yi hakan domin addu'a ita ce makamin bawa.
Alhaji Aliyu yace duk mai kishin kasar ya damu da ita. Yace tun da aka fara azumi kuma wasu sun ce 'yan Boko Haram Musulmai ne to suna ganin albarkacin watan Ramadana zasu daina tashin tashinanr da su keyi amma maimakon su daina sai ma kara kaimi suka yi. Sabili da wannan ya sa suka ga yakamata su hada kan jama'a a yi addu'a domin a nemi zaman lafiya. Daga zaman lafiya ake samun komi a rayuwa.
Taron addu'ar ya samu halartar manya-manyan malamai da shugabanni daga sassa daban daban cikin jihar. Sarkin Agege Alhaji Musa Dogonkade ya yi nasiha a wajen addu'ar. Yace babu abun da suka sa a gaba illa addu'a.
Shi kuma na'ibin limamin masallacin Sheriff Isma'il cewa yayi kashe-kashen bai takaita ga musulmai ba kurum kuma yana kira ga 'yan Najeriya mabiya addinai daban daban da su yi hakuri da juna.
Shugaban matasa Ibrahim Garba Tafida kira yayi ga daukacin matasan kasar da su gujewa shiga aikin ta'adanci domin kashe-kashen da su ake yin anfani. Idan matashi yana karatu yana kuma sana'a ba za'a iya yin anfani dashi ba kuma ba za'a sameshi wajen wani mugun aiki ba.
Ga rahoton Ladan Ibrahim Ayawa.
Your browser doesn’t support HTML5