Gagarumin aikin sintirin da jami’an tsaro suka kaddamar a makwanni biyun da suka gabata a birnin Yamai ne ya bada damar cafke mutane maza da mata kimanin 20 cikinsu har da mai gadin wata makarantar firamare da ake zargi da tare mutane akan hanya domin kwacen babura ko jakar hannu da wayoyin salula.
Gamsuwa da wannan aiki na ‘yan sanda ya sa ministan cikin gida Bazoum Mohammed kai masu ziyara.
Matsalar tsaro a birnin yamai wani abu ne da sau tari ya kan haifarda asarar rayukan bayin Allah da suka kuskure tirjewa ‘yan fashi.
Ku Duba Wannan Ma Kotu Ta Yankewa Wasu Sojoji Hukuncin Laifin Fyade a Sudan Ta KuduJama’a sun yabawa jami’an tsaro saboda dagewarsu wajen kare mutane da dukiyoyinsu a wannan lokaci da yawaitar amfani da kayan maye a wurin matasa ke jefasu cikin miyagun aiyuka dalili kenan da wannan magidanci ke kiran hukumomi su hukunta dukkan wadanda aka kama da laifin tayarda hanakalin jama’a.
A cewar ministan cikin gida, motoci a kalla 60 shake da jami’an tsaro ne ke kewaya birnin Yamai a kulliyaumin da nufin kare jama’a da dukiyoyinsu saboda haka ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu.
Your browser doesn’t support HTML5