An Yi Mummunan Ta'adi Sakamakon Zanga Zanga a India

An kashe mutum daya a rikicin da ya barke a arewa maso gabashin Indiya a yau Alhamis yayin zanga-zangar adawa da sabuwar dokar tarayya da za ta ta yi sassauci ga wasu tsiraru ciki har da Musulmai daga wasu kasashe makwabta, 'wajen ba su yancin zama 'yan kasar India.

Narendra Modi

Firai minista Narendra Modi, ya ce dokar da za ta yi kwaskwarima ga dokar zama dan kasa, wanda majalisar dokoki ta amince da ita a ranar Laraba, an yi ta ne domin kare tsirarun kabilu daga Bangladesh, Pakistan da Afghanistan.

Amma dubban masu zanga-zanga a jihar Assam, wadanda ke da iyaka da Bangladesh, sun ce matakin zai bude yankin ga ambaliyar masu shigowa da bakin haure daga kasashen waje.

Wasu kuma sun ce babbar matsalar sabuwar dokar ita ce ta saba wa tsarin mulkin Indiya ta hanyar ba da kariya ga Musulmi.

'Yan sanda a babban garin Guwahati na Assam, sun harba harsashai da hayaki mai sa hawaye kan gungun masu zanga-zangar, amma wasu da dama sun yi zanga-zanga a kan tituna.