An Yi Garkuwa Da Matan Wani Mutun Su Biyu, A Garin Kalmalao

Wasu 'yan fashi ne suka yi awon gaba da matan wani bawan Allah a kauyen Kalmalao.

Wadansu mutane dauke da bindigogi su kimanin mutum 7, sun yi garkuwa da mata 2 iyalan wani mutum. bayan sun abka wa gidansa a garin Kalmalao da ke Karamar Hukumar Illela a jahar Sokoton Najeriya. Garin na Kalmalao dai na kan iyaka ne da Birni N'Konni na Jamhuriyar Nijar - wanda gonaki ne kawai ke iyaka da karamar hukumar mulkin Illela ta jihar Sokoto da Birnin N'Konni.

Maharban sun share tsawon lokaci, suna barin wuta a cikin garin don tsoratar da mutanen Kalmalao don hana su fitowa tunkarar su. Malam Mahamadu, shi ne a kayi awon gaba da matansa biyu.

Yana mai cewa: da misallin karfe 3:00 na tsakar dare ne ya ji 'yan fashin su na takaddama da yaransa da suke bakin gida, suna tambayyar su inda maigidan yake, daga jin haka sai ya samu ya haura ta katanga ya arce.

Tserewar da yayi ta kubutar da shi, amma yanzu haka iyalansa suna hannun masu garkuwar, bashi da masaniyar halin da suke ciki.

Daya daga cikin yaran gida ya shaida wa Muryar Amurka cewa: Ya ga 'yan fashin lokacin da suka shiga cikin gidan, suka tara matan mutumin, suka tambaye su yana ina, matan dai sun bayyana cewar basu da masaniyar inda yake. Amma sun tasa keyayar matan biyu, basu tafi da yaro ko daya ba,

Haka zalika, makwabcin Malam Muhammadu, wanda aka yi awon gaba da matansa biyu, ya shaida cewar sun ji harbe-harben bindigogi, lokacin da lamarin ke faruwa, amma ba su iya kai wani agaji ba, saboda tsoron kada su fada cikin wani hali.

Ga rahoton Harouna Mammane Bako, a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Yi Garkuwa Da Matan Wani Mutun Su Biyu, A Garin Kalmalao