Masu garkuwa da mutane, sun kai hari wani asibiti a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya, inda suka yi awon gaba da ma’aikatan jinya biyu.
Lamarin ya faru ne a babban asibitin Idon da ke da tazarar tafiyar kasa da kilomita daya da wani shingen binciken ‘yan sanda akan hanyar Kaduna zuwa Kachia.
Wannan lamari na faruwa ne sa'o'i bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari a Jami’ar Greenfield da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda rahotanni suka ce an sace dalibai da dama.
Shugaban karamar hukumar Kajuru Cafra Casino, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, ya nemi jam’a su kwantar da hankalinsu.
Rahotanni sun ce da sanyin safiyar ranar Alhamis maharan suka far wa asibitin yayin da wasu ke cewa a daren Laraba lamarin ya auku.
Gwamna Malam Nasir El Rufai, ya ce gwamnatinsa ba za ta biya kudin fansa ba, kuma ba ta da shirin yin sulhu da ‘yan bindigar kamar yadda wasu jihohi ke yi.
Rahotanni na nuni da cewa har yanzu akwai ragowa daga cikin dalibai 39 da aka sace a kwalejin nazarin ilimin gandun daji da ke Afaka a jihar ta Kaduna, wadanda aka sace tun farkon watan Maris.
Matsalar garkuwa da mutane, ta zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya, lamarin da ya sa aka yi ta rufe makarantu, mutane suka kauracewa gonaki da manyan hanyoyi da ke yankin.