An Yi Garkuwa Da Ma'aikata 'Yan Kasar China 3 A Jihar Nejan Najeriya

Najeriya

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aikata ‘yan kasar China uku da ke aikin gina madatsar ruwa dake tsakiyar Najeriya, tare da kashe wasu ma’aikatan guda biyu 'yan Nigeria, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a ranar Alhamis.

Maharan sun kai harin nekan ma’aikata dake aikin “SinoHydro” a jihar Neja a ranar Talata da yamma, a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Wasiu Abiodun a wata sanarwa da ya fitar.

Mista Abiodun ya ce, “Rundunar ‘yan sandan da ke aiki a wurin sun yi artabu da harbe-harbe da masu laifin, an kubutar da wasu ‘yan kasashen waje hudu, amma daya daga cikinsu da wasu ma’aikatan yankin biyu an harbe su tare da raunata su."

Daga baya ma’aikatan biyu sun mutu a asibiti.

“A yayin wannan fadan, an sace wasu ‘yan kasashen waje uku a lokacin da suke kokarin boyewa,” in ji sanarwar.

A wannan kasar da ta fi yawan mutane a Afirka, ‘yan bindiga masu aikata laifuka sukan kai hari kan ma'aikatan kasashen waje da ke aikin samar da ababen more rayuwa don neman kudin fansa.

An sha kai wa ma’aikatan kasar Sin hari sau da dama a Najeriya a ‘yan watannin nan, yayin da suke gudanar da ayyukan samar da ababen more rayuwa na biliyoyin daloli da suka hada da ma’adanai, da layin dogo, da filayen jiragen sama da kuma hanyoyi.

Koda yake hukumomi ba safai suke tabbatar da biyan kudade ba, amma galibi ana sakin wadanda abin ya shafa ne bayan an biya kudin fansa.

-AFP