WASHINGTON, D.C. —
Rahotanni daga jihar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, wasu ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, sun yi garkuwa da dan majalisar dokokin jihar Hon. Bashir Muhammad Bape da ke wakiltar mazabar Nguroje.
Bayanai sun yi nuni da cewa ‘yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a gidan dan majalisar da ke Jalingo suka yi awon gaba da shi.
Kakakin ‘yan sandan jihar DSP David Misal, ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, ya kuma yi kira ga jama’a da su taimaka wajen ba da bayanan da za a ceto dan majalisar.
Wannan shi ne karo na biyu da ake sace dan majalisa a jihar ta Taraba.
Wannan na zuwa ne yayin da matsalar garkuwa ke gagaran kundila, batun da masana ke dangantawa da shakulatin bangaro daga gwamnatin kasar.