An yi zagaye na biyu na gangamin jaddada muhimmancin amfani da bayanan ililimin kimiyya a jiya Asabar, a Dandalin Kasa na National Mall da ke birnin Washington DC, kuma an yi makamantan irin wannan gangamin har guda 200 a sassan duniya.
Dubban mutane ne su ka halarci wanda aka yi a birnin Washington DC, to amma yawansu bai kai na bara ba.
Macin na jiya Asabar ya faru ne bayan da bangaren kimiyya ya galabaita a karkashin gwamnatin Shugaba Donald Trump. Sauye-sauyen da su ka shafi bangaren na kimiyya sun hada da janyewar da Amurka ta yi daga yarjajjeniyar Paris kan hanyoyin dakile canjin yanayi da kuma goyon bayan da Shugaba Trump ke bai wa amfani da makamashin kwal. Haka zalika, gwamnatin ta Trump na shirin soke ka’idojin da aka gindaya na dakile gurbatar muhalli.