Su dai wadanda suka yi artabu da jami’an tsaron na zaune ne a unguwar ta Keke-B, kimanin shekaru uku kennan ba tare da an san akidar su ba.
Mazauna unguwar wadanda suka so a sakaye sunayensu sun bayyana abubuwan da suka sani.
“Jiya da daddare muna kwance a cikin gida, sai muka ji harbi. Muka ce me yake faruwa? Bamu sani ba, sai aka ce sojoji ne. Muka leka muka ga ana ta guje-guje ana ta zagaye gidaje. Misalin kamar karfe biyar lokacin da ake Sallah sai suka ce ‘duk wanda bai fita ba, nan da mintuna ishirin ya rasa ranshi.’ Sai na bude kofa kawai. Ina bude kofa sai na fita, sai suke tare ne sojoji suke ce in fito da yara da mata duk. Da gari ya waye, sai suka yi mana bayani cewa ‘ai ‘yan Boko Haram ne a nan gidan’. Bamu yi bacci ba jiya sam-sam” a cewar wani wanda ya so a sakaye sunanshi.
To ko yaya jami’an tsaron suka yi wajen kawo wannan sumame? Alhaji Suleiman Muhammad shine Dagacin unguwar Keke-B.
“Da safiya tayi, shine na zo wurinsu (jami’an tsaro) nace ya akayi? Shine suka yi mun bayani, suna nuna mun. Mu abunda suka yi mana, sun zo mana taimako ne. Da mun san da irin wadannan, tuni mu ya kamata mu je mu bada report, mu dauki mataki domin a yi mana maganinsa. Muma tsoron su muke ji.
Tuni dai jami’an tsaron da Sashen Hausa na Muryar Amurka ya iske a wajen ginin da ya sha batakashi sun tabbatar da cewa an hallaka jami’in soja yayin da jami’in SSS ya ji rauni a hannu.
Sai dai duk kokarin VOA na jin ta bakin darektan yada labaru na rundunar soji dake Kaduna Kanal Abdul Usman bai yi nasara ba.
Your browser doesn’t support HTML5