An Yi Amfani Da ‘Yan Banga A Zabukan Karshe - Inji E.U. -

Yanzu haka wani rahoto da masu saka ido daga kungiyar Tarayyar Turai (E.U.) suka fitar ya yi zargin cewa an ci zarafin masu jefa kuri'a tare da firgita su a zaben gwamnoni da aka kammala a jihohin Bauchi, Biniwai, da kuma Kano.

Tawagar masu duba zabe ta kungiyar Tarayyar Turai ta fitar da rahoto kan kammala zabe da aka gudanar a jihohin Bauchi, Biniwai da kuma Kano. Ta ce an samu matsalar 'yan banga.

Jami’ar yada labarai ta Tarayyar Turai, Sarah Fradgley, ta fitar da sanarwa tana cewa ‘yan banga sun hargitsa zaben ta hanyar firgita masu kada kuri’a da ma cin zarafinsu.

Tunda farko shugabar tawagar Maria Arena, ta ce aikin tawagar shi ne su tabbatar da gaskiya ba tare da nuna bangare a zaben ba.

Sannan kuma ta ce ba su da ra’ayi kan jam’iyya ko wanda zai lashe zabe, kuma za su tabbatar da cewa an yi adalci da kuma gujewa wannan yanayi na banga.

Masu duba zabe na cikin gida suma sun nuna matukar damuwa ga yadda aka samu illar ‘yan banga da ‘yan siyasa su ka yi amfani da su don lashe zaben ta hanyar ko a mutu ko ayi rai.

Yanzu dai za a jira a ga yadda lamarin bangar da shi ne dalili tun farko da yasa soke zaben da aka kammala, ko zai yi tasiri wajan shari’a a kotuna tun da hukumar zaben ta ayyana wadanda su ka lashe.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Rohoton EU Yayi Zargin Amfani da ‘Yan Banga A Zaben Gwamnoni Da Aka Kammala