Kimanin mayakan Hoko Haram 125 ne aka sallama a yayin wani buki na musamman da aka shirya a sansanin tsofafin ‘yan kungiyar dake garin Goudoumaria na yankin Diffa, bayan da aka yi amanar cewa sun watsar da mummunar akidar da suka koya daga kungiyar ta Boko Haram a can baya,
domin jaddadawa duniya cewa sun tuba daga dukkan wata aika aika.
Wadannan matasa sun yi rantsuwa akan alkur’ani mai tsarki abin da ya sa ministan cikin gida Bazoum Mohamed yi masu huduba.
A watan disambar 2016 ne aka kafa wannan sansani da nufin koyawa mayaka 235 wadanda suka tuba daga Boko Haram sana’oin dogaro da kai. Shekaru uku bayan kaddamar da wannan shiri matasan wadanda suka hada da ‘yan kasashen Nijer da Najeriya sun yi godiya da samun abin da suka kira matakin sake mayar da su kan hanyar gaskiya.
Wakilin Gwamnan Borno a wajen wannan buki Alhaji Cugun Mele ya bayyana farin ciki da ganin wannan rana.
Ministan cikin gida Bazoum Mohamed, ya gargadi al'umma da su rungumi matasan da hannu biyu biyu kafin ya yi kira ga sauran ‘yan kungiyar Boko Haram da su dawo gida.
Jakadan Amurka a Nijer Eric P. Whitaker ya halarci wannan buki dake baiwa matasa kimanin 125 damar bankwana da aiyukan ta’addanci ta hanyar wannan shiri na hadin gwiwar kungiyar PNUD ko UNDP da gwamnatin jamhuriyar Nijer da kungiyar Tarayyar Turai.
Ga karin bayani a sauti: