Tsoffin mayakan Boko Haram da aka yaye sun dauki alkawarin zama 'yan kasa na gari yayin da aka yi bikin yaye su..
Tsoffin mayakan da suka mika kai sun samu horaswa na tsawon makonni 16 wadda gwamnatin tarayya ta dauki alhakin shiryawa tare da horasa dasu sana'o'i daban daban.
Kwararru da kuma masana da malaman addinin musulunci suka wa'azantar dasu da tsarkakesu ta hanyar cire masu tsatsauran ra'ayi domin mayar da su garuruwansu na asali.
Daya daga cikin wadanda suka samu horon ya yi jawabi inda ya godewa gwamnatin tarayya akan horon da aka basu da kulawa dasu da horas dasu sana'o'i daban daban domin samun dogaro ga kai yayinda suka koma wurarensu na asali. Ya roki mutanen dake waje da su yi hakuri dasu, su yafe masu abubuwan da suka wuce. Ya yi fatan duk 'yan Boko haram da shugabansu Abubakar Shekau zasu tuba wata rana.
Gwamnan Gombe Alhaji Hassan Ibrahim Dankwambo shi ya yi jawabi a madadin gwamnaonin jihohin arewa maso gabashin kasar. Bayan ya roki al'ummar kasa su karbi wadannan tubabbun, ya ba tsoffin mayakan tabbacin cewa yanzu daidai suke da kowane dan kasa. Injishi babu wanda zai nuna masu wani bambanci.
Daga karshe an mika mutanen ga gwamnonin jihohinsu domin su mayar da su garuruwansu na asali.
Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5