Hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Sadique Abubakar ya marabci tawagar hafsan hafsoshin sojojin saman Liberia kasar da ita ma tana da dalibai cikin wadanda aka yaye a bikin.
Yayin da yake jawabi, Air Marshall Abubakar ya ce a wannan karnin na 21 ana samun yawan tashin hankali da sautari neman iko irin na siyasa ke haddasasu.
Ya kara da cewa, baya ga haka, ta'addanci da tsageranci na samun gindin zama, tun bayan karshen yakin cacar baka a duniya.
Air Marshall Abubakar ya ci gaba da cewa Rundunar sojin saman Najeriya na ci gaba da taka rawa a ciki da wajen kasar.
A yanzu haka, tare da hadin gwuiwar sauran jami'an tsaro ya ce suna can suna kai farmaki akan 'yan ta'addan Boko Haram.
Da yake maida jawabi ministan tsaron Liberia Manjo Janar Daniel Zankai ya tuna da irin rawar da Najeriya ta taka wajen wanzar da zaman lafiya a kasarsa.
Ya tuna da sadaukarwar da Najeriya ta yi da kayan aiki da jami'anta.
Zankai ya ci karan-kansa ya amfana da kwamandojin Najeriya yayin da yake rike da mukamin hafsan hafsoshin sojojin kasarsu.
Kyftin Abdulkarim Nuhu, shugaban makarantar koyas da tukin jiragen sama na yaki ta kasa da kasa dake Ilorin inda sojojin da ake yaye wa suka kammala karatunsu, ya ce makarantarsa ita ce irinta daya tilo a duk fadin Afirka da ke horas da matukan jiragen yaki na sama.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5
.