A wani al'amari mai janyo takaddama da fassari iri iri, wato kotu a China ta yanke ma hamshakin mai kudin nan kuma dan siyasa, Ren Zhiqiang daurin shekaru 18 a gidan yari.
WASHINGTON, DC —
Wani attajiri dan China, tsohon mai harkar gine-gine, wanda ya soki Shuganan China Xi Jinping kan yadda ya tinkari matsalar COVID-19, ya samu hukuncin daurin shekaru 18 saboda laifin almundahana.
Wata sanarwar da matsakaiciyar kotun Beijing Ta Biyu ta yi yau dinnan Talata, na cewa an samu Ren Zhiqiang dan shekaru 69 da laifin handame wajen $16 mallakin wani kamfani gwamnati da ya taba shugabanta, baya ga bayar da cin hanci da kuma amfani da iko ba bisa ka’ida ba, wanda ya janyo ma kamfanin asarar dala miliyan 17.
Kotun ta ce Ren ya amsa cewa ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da yi, kuma ba zai ma daukaka kara ba. Baya ga wannan hukuncin da aka yanke masa, an kuma ci shi tarar dala sama $600,000.