Shekara hudu da suka gabata ne dai yan sanda suka kama Peter Nielsen, dan shekaru 54 a duniya da laifin kashe matar sa mai suna zainab da niyar sa Petres a gidan su dake legas.
Kotu tace bisa hujjojin dake gaban ta na yansanda masu bincike dana likita ya nuna cewar Peter ne ya shake su har suka mutu, don haka hukuncin sa shine hukuncin kisa ta hanyan ratayewa.
Masu fafutukar kare hakkin bil adama da ma ne dai suka matsa na ganin an hukunta Peter duk da cewar ba dan Najeriya bane, amma kuma a Najeriya ya aikata laifin.
Dr Joy Odumakin mai fafutukar kare yancin mata a Najeriya na daya daga cikin su da ta yaba da hukuncin kotun bayan shariar shekaru hudu, kamar yadda ta shedawa yan jarida a harabar kotun a Legas.
Yanzu haka dai yan najeriya da dama ne dai ke zaman hukuncin kisa a gidajen yarin Najeriya ba tare da Gwamnonin da doka ta amince da sanya hannun su kafin aiwatar da hukunci ba, ke kin sanya hannun, don haka a karshe ke bigewa da tamkar hukuncin daurin rai da rai ne aka yanke.
Sai dai yanzu abun jira a gani shine ko Denmark zata bukaci musayar fursuna tsakanin ta da Najeriya domin bada dama a maida dan Denmark din kasar shi ta asali.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5