Wata kotu a Mali ta yanke hukuncin kisa ma wani mai ikirarin jihadi da ake zargi, da kuma wani da ake tuhumarsu tare da kashe mutane fiye da dozin biyu a hare hare kan ‘yan kasashen waje a 2015.
WASHINGTON, D.C. —
Hukuncin na jiya Larabara akan Fawaz Ould Ahmed da Saou Chaka na zuwa ne bayan kwanaki biyu na sauraron shari’ar.
Ahmed ya ce kungiyarsa ta Al-Mourabitoune ita ta kai harin a kulab din La Terrasse, amma bai nuna nadama saboda kashe mutum 5 a matsayin ramuwar gayya na zane batanci da mujallar Charlie Hebdo ta yi ga annabi Muhammadu (S.A.W) ba.
Ahmed ya kuma amsa cewa ya taka rawa a harin da ya kashe mutum 17 a Otel din Byblos a garin Sevare a watan Agusta da kuma wani da ya kashe mutum 20, ciki har da ‘yan kasashen waje 14, a otel din Radisson Blu a Bamako a watan Nuwamba.