Wata kotu a Jamhuriyar Benin ta yanke hukunci wa ‘yan wasan kwallon kafar kasar su 10, dake cikin tawagar 'yan kasa da shekaru 17, zuwa gidan maza saboda samun su da laifin yin karya dangane da ainihin shekarunsu na haihuwa.
Kotun wadda take zamanta a birnin Kotono, ta yankewa 'yan wasan hukuncin daurin wata guda ne wa kowannensu.
A watan Satumba ne dai aka kame 'yan wasan wanda suke ikirarin cewa, shekarun su na haihuwa kasa da 17 ne, bayan an gano cewar karya ce kawai suka sharara, wanda hakan yasa aka kore su daga cikin wasan neman tikitin halartar shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa sakamakon an musu gwajin kashi (MRI).
A shekarar 2004, hukumar ce idan ba'a mantaba ta FIFA ta taba haramtawa Jamhuriyar Benin shiga wasanni, saboda matsalolin cin hanci da rashawa da suka yiwa hukumar kwallon kafar kasar katutu.
Haka zalika tsakanin shekarar 2010 zuwa 2013, hukumar kula da wasan kwallon kafa ta FIFA, ta sha yiwa kasar gargadi da barazanar sake daukar matakin haramta mata shiga dukkanin wasanni, muddin ta gaza wajen gyara matsalolin da ke yiwa harkar kwallon kafa karan tsaye.
Wannan hukumcin ya hada da jami'an gudanarwa na manyanan 'yan wasan.