An Yanke Hukumcin Daurin Rai Da Rai A Kan Umar Faruq Abdulmutallab

Umar Faruk Abdulmutallab a Kotu

Abdulmutallab ya amsa laifin tuhumar da aka yi masa ta kokarin tayar da bam cikin wani jirgin saman fasinjar Amurka a 2009

An yanke hukumcin daurin rai da rai a kan matashin nan dan Najeriya da aka tuhuma da kokarin tayar da bam a cikin wani jirgin saman fasinjar Amurka a ranar kirsimetin 2009.

Yau alhamis a birnin Detroit dake Jihar Michigan aka yanke wannan hukumci a kan Umar Faruk Abdulmutallab.

A watan Oktoba ya amsa laifin a daidai lokacin da aka fara gudanar da shari'arsa. ya fadawa kotun cewa ya dauki matakan ne a zaman ramuwar gayyar abinda ya kira karkashe Musulmin da ba su ba, ba su kuma gani ba a Yemen da Afghanistan da wasu wurare.

Masu gabatar da kara sun ce Abdulmutallab yayi niyyar yin shahada ce kuma dalili daya kawai ya sa ya shiga wannan jirgin saman kamfanin Northwest Airlines: watau ya kashe dukkan mutane 290 dake cikinsa a wani bangare na aikin da al-Qa'ida ta sa shi.

Laifuffukan da aka tuhume shi da aikatawa sun kunshi hada baki domin aikata ta'addanci, da kokarin yin amfani da makamin kare dangi a saboda kokarin da yayi na tarwatsa wannan jirgi da ya taso daga Amsterdam a ranar 25 Disamba 2009.

Aika Sharhinka