Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata alkalin kasar Amurka ta sallami mai taimaka mata yanke hukunci a shari'ar Abdulmutallab


Umar Faruk Abdulmutallab a wani hoton da aka zana a kotu.
Umar Faruk Abdulmutallab a wani hoton da aka zana a kotu.

Wata alkalin Amurka ta sallami daya daga cikin mutanen da suke taimakawa alkali yanke hukumci a shari’ar dan Najeriyan nan da ake zargi da yunkurin tarwatsa jirgin sufurin Amurka, ta wajen boye nakiya a cikin wandonshi a shekara ta dubu biyu da tara.

Wata alkalin Amurka ta sallami daya daga cikin mutanen da suke taimakawa alkali yanke hukumci a shari’ar dan Najeriyan nan da ake zargi da yunkurin tarwatsa jirgin sufurin Amurka, ta wajen boye nakiya a cikin wandonshi a shekara ta dubu biyu da tara.

Alkalin dake Detroit Nancy Edmunds ta salami macen ne ‘yar asalin Najeriya daga kasancewa daya daga cikin mutanen da zasu taimaka mata yanke hukumci jiya alhamis, ‘yan mintoci bayanda masu shigar da kara da kuma laiyoyin dake kare Abdulmutalab suka amince da zaben mutane goma sha biyu, da kuma wadansu hudu da ke zaman jiran tsammani. Edmunds tace akwai matsala da macen sai dai bata yi karin haske a kai bai.

Lauyoyi masu shigar da kara da kuma masu kariya sun shafe kwanaki biyu suna yiwa sama da mutane arba’in tambayoyi yayinda suke zaben wadanda zasu taya alkali yanke hukumci a shari’ar Umar Farouk Abdumutallah, wanda aka ba lakabi “dan harin kamfai” ko kuma underwear bomber. Nan da nan suka zabi mutane 12 da kuma masu jiran tsammani guda hudu ba tare da bayyana damuwa kan kasancewar daya ‘yar Najeriya ba.

Dokokin kotu sun bukaci a maye gurbinta da daya daga cikin masu jiran tsammani a kuma sake zaben wani a madadinshi. Za a fara gabatar da karar ranar 11 ga wannan wata na Oktoba.

Abdulmutallab ya yi ta tada jijiyar wuya a kotu ranar Talata lokacin da ake zaben mutanen da zasu taimakawa Alhaki yanke hukumcin, yana bayyana cewa, yana da alaka da kungiyar al-Qaida yayinda kuma yake cewa malamin nan haifaffen Amurka Anwar al-Awlaki har yana nan da rai. Amurka da kuma jami’an kasar Yemen sun ce an kashe Awlaki a wani harin sararin sama da aka kai a Yemen makon jiya.

XS
SM
MD
LG