Wannan mataki na zuwa ne kwanaki takwas bayan da aka rantsar da sabuwar gwamnati a karakashin jam’iyyar APC.
“Duk ci gaba da za mu samu, idan ba mu yi maganin wannan ba, ci gaban mu bai kai ba dole mu kare rayukan al’uma, saboda haka muka ga cewa ya kamata mu fito da wannan tsari na gyara muhalli.” Ganduje ya ce da aka tambayeshi maksudin wannan tsari.
Ya kara da cewa wannan tsari ba na wani dan lokaci ba ne zai ci gaba da zama dawwamamme, ya na mai cewa za a karawa hukumar da da alhaki kwashe shara karfi domin ta dinga kwashe shara ma har da daddare bayan da rana.
A cewar Ganduje, ita kanta sharar za a san yadda za a sarrafa ta ta zama taki ga manoma ta hanyar hadin kai da kamfanoni masu zaman kasu.
“Abin da gwamnati ta yi na wannan shara ya yi daidai, saboda a tsabtace muhalli, a kuma ciccire wasu datti da ke cikin kwata.” Inji wani mazaunin jahar ta Kano.
Ga karin bayani a rahoton Baraka Bashir:
Your browser doesn’t support HTML5