An Tura ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Zuwa Yankin Biafra

FILE - A man carries the Biafran flag during a parade in Ekwe village, near Enugu in southeastern Nigeria, May 27, 2008.

Cikin wata sanarwa da ta fito daga kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Ola Bisi Kolawole, tace insufeta janar na Najeriya Mr. Solomon Arase ya bada umarnin tura karin ‘yan sandan kwantar da tarzoma cikin ‘damara, zuwa yankin kudu maso gabashin Najeriyar.

Hakan ya biyo bayan cigaba da karuwar aikace aikacen tashin hankali na matasan kabilar Igbo, dake fafutukar ballewa daga tarayyar Najeriya. Dr Mohammed Elur Dangir wanda yake kwararre kan sha’anin tsaro yace, idan har ba haka ba akayi kuma aka barsu suka sami nasara to zasu ci gaba ne har abin yazo yafi karfin gwamnati.

Shugaban ‘yan sandan Najeriya yace rundunar ta lura masu rajin kafa kasar Biafra, nayin babbar barazana ga tsaron kasa. Masana irin su Dr Abari na ganin dacewar wannan umarni na shugaban rundunar Najeriya, inda yace zanga zangar da akeyi domin neman a raba kasa, wanda wanann kuwa ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa, kuma cin amanar kasa ne daga duk wanda ya nemi haka.

Tuni dai har hedikwatar ‘yan sandan Najeriya ta umarci mataimakan Sufeta janar na ‘yan sandan kasar guda uku dake shiyyoyin Benin da Calabar da Umuahia, da suyi amfani da karfin tsiya don shawo kan masu wannan fafutuka.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tura ‘Yan Sandan Kwantar Da Tarzoma Zuwa Yankin Biafra 1'53"