Dokar ta baiwa kamfanoni masu zaman kansu damar tafiyar da harkokin fansho kana gwamnati ta ja baya daga biyan fansho ga ma'aikata.
Sabuwar dokar ta shafi wadanda suka yi ritaya ne daga shekarar 2004 zuwa yanzu.
Amma su 'yansandan da suka yi ritaya sun ce gwamnatin Najeriya suka yiwa aiki ba wata kamfani ba daban. Babu hujjar kaisu wani kamfani a ce shi ne zai biyasu. Wadanda suka yi ritaya kafin dokar ana biyansu yadda ya kamata amma su ba'a biyansu haka.
Yadda aka cire sojoji da SSS daga sabon shirin haka ya kamata a cire 'yansanda daga shirin musamman idana aka yi la'akari da cewa rundunar 'yansanda ce ta haifi SSS, wato 'yansandan fararen kaya kamar yadda A. C.Tijjani Abdulkadiri shugaban kungiyar 'yansandan ya sanar..
Wani da yayi ritaya yace kashi daya cikin kudadensa aka biyashi. Da kashi hamsin ake biya idan mutum ya yi ritaya. Hatta kudin asibiti sai da ya sayarda motarsa ya biya. Yana da 'ya'ya 28 da mata biyu amma a duk wata nera dubu 30 ake biyansa. Yana da kudi da kamfanin fansho kusan nera miliyan biyar amma idan wata ya kare dubu 30 suke biyanshi.
Ga karin bayani.