An Tuhumi 'Yan China 22 Da Shigo Da Kayan Jabu Amurka

Gwamnan New York Andrew Cuomo

Wata kotu a New York ta tuhumi wasu 'yan China 22 da yin fasakwaurin wasu jabun kaya zuwa nan Amurka

Wata kotun tarayya a birnin New York, ta tuhumi wasu ‘yan kasar Sin su 22 da laifin fasakwaurin jebun wasu kayayyaki zuwa nan Amurka, wadanda aka yi kiyasin kudinsu zai kai kusan dalar Amurka rabin biliyan.

Kayayyakin na bogi, sun hada da kayan kawa da suka yi fice, kamar na jakar Louis Vuitton, da jakar adana kudi a aljihu da aka fi sani da wallet ta Michael Kors da kuma turaren Chanel.

A jiya Alhamis aka cafke mutane 21 da ake zargi da hannu a wannan almundahana.

Attorney Janar na Amurka, ya ce wadanda ake tuhumar, ana zarginsu ne da fasakwaurin kayayyakin da aka hada a China, wadanda na bogi ne, da aka shigo da su kasar cikin kwantena-kwantena, a matsayin ingantattun kaya, aka kuma sauke su a tashoshin ruwan New York da New Jersey.

Baya ga tuhumar da ake musu ta shigar da kayan bogi, ana cajin mutanen da laifukan boye kudaden haram da yin almundahana a fannin shige da fice a Amurkan.