A jiya ne aka tuhumci wasu mutane da suka hada sojojin Amurka shidda da wasu fararen hula da laifin satar kayan aiki da makamai na rundunar sojan Amurka da kuma sayar da su ga wasu mutanen kasashen ketare da suka hada da China, Rasha da Ukraine.
WASHINGTON, DC —
Kayan da aka sace din sun hada da na’urorin hangen nesa na maharba, kayan hadi na manyan bindigogin iggwa, sulkuna da kuma maganadisun tayarda nakiyoyin gurneti.
Bayanan da aka gabatar a kotun ta jihar Tennessee sunce su sojojin 6 ne suka sato kayan, suka mika su ga wasu mutane biyu fararen hula, wadanda su kuma suka tallata su ta hanyar kampanin e-bay mai sayarda haja a cikin duniyar gizo ta internet.
Wadanda suka sayi tarkaccen kayan, ko bayan mutanen Rasha, China da Ukraine, har ila yau sun hada da mutanen kasashen Malaysia, Kazakhstan da Mexico.