Alkali ya watsar da tuhumar da ake yiwa wani musaki na laifin daukar bindiga ba tare da izini ba, a jihar New Jersey dake Amurka.
Jami’ai dai sunce ‘yan sanda sun tare mutumin mai suna Hubbard tare da abokansa uku cikin mota alokacin da suka ki bin umarnin wutar kan titi mai bada hannu, bayan da aka tare su ne cikin motar kuwa jami’an tsaro suka sami karamar bindiga cikin motar. An tuhumi duk fasinjojin dake cikin motar da laifin rike bindiga ba tare da izini ba bayan da kowa ya musunta cewa bindigar sa ce.
Hubbard dai ya shafe watanni hudu a ‘daure, daga bayane Lauya mai kare shi ya kira lamarin a matsayin abin mamaki, domin shi Hubbard nada nakasa a hannun sa sanadiyar hatsarin mota da ya samu a baya, kuma bazai iya yin amfani da hannun sa ba. jin haka ne yasa Alkali ya kori tuhumar da ake masa.