Masu yin sharhi akan alamuran mulki da siyasa sun fara tsokaci akan jinkirin nada Kwamishinoni a jihar Neja, Alhaji Shehu Musa Tanko, yace samarda Kwamishinonin zai sa aiyukan raya kasa su ci gaba kamar yadda ake bukata.
Ya kara da cewa nada Kwamishinoni zai sa aiki ya ci gaba domin suna da alaka da ‘yan siyasa ba kamar Sakatarorin din din din ba na ma’aikatun Gwamnati.
Shi kuwa tsohon dan majalisar wakilan Najeriya, Bala Adamu Kuta, yace bisa la’akari da yadda sabuwar Gwamnatin APC, ta sami dinbin baki daga jam’iyyar PDP, dole ne Gwamna Abubakar Sani Bello, yayi karatun ta natsu.
Shugaban jam’oiyyar APC, a jihar Neja, Injiniya Muhammad Imam, yace muddin hakan bai sabawa tsarin mulkin kasa ba toh ai ba wani illa bane. Yana mai cewa Gwamnana nada hurumin yayi shi duk ta yadda ya ga za’a samu Nasara, baiwa dan mutane na korafe korafe ba.