An tsinci jakar leda ‘dauke kudi har dala dubu sittin da uku kimanin naira miliyan goma sha biyu da dubu dari shida, a wani gurin shakatawa na jihar Pennsylvania.
‘yan sanda dai sunce wani mai ziyara ne yayi wannan tsuntuwar a ranar asabar, an kuma sami wasu takardu cikin jakar da take nunin cewa wata mata ce ta mallaki kudin, dama wasu bayanai da zasu taimaka wajen neman matar.
Jami’an dai sunce matar ta kai rahotan cewa kudin ta sun bace kusan shekara guda kenan da ta wuce, amma yanzu haka matar ta bar garin batare da barin lambar waya ko adireshin yadda za’a same ta ba. ‘yan sanda dai na ta kokarin neman matar domin mayar mata da dukiyar ta.