WASHINGTON, DC —
Biyo bayan rashin nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Stoke City tayi a jiya, inda ta shan kashi a hannun kungiyar Swansea City, inda aka tashi wasan biyu babu ko daya.
Manajan kungiyar ta Stoke City, Mark Hughes, ya ce da alamar wuya kungiyar ta kasance ta takwas a primiya lig, saboda kashin da kungiyar ta sha a hannun Swansea City.
Ya kara da cewar kungiyar tasa tayi sakaci na rasa wannan wasan da ace kunnan doki akayi, da Stoke City ta kasance ta takwas aka teburin inji Mark Hughes.
Yace kungiyar ta Stoke City, ta yiwa ‘yan kungiyar Swansea City, wani gani-gani da kuma daukar ta kanwar lasa amma suka sha mamaki.