An tsare wani mutum dangane da fashe fashen da suka yi sanadin asarar rayuka a Najeriya

Hayaki da baraguzai sun turnuke sararin samaniya. jim kadan bayan tarwatsewar bom a wata mota kusa da 'yan kwana kwana da suka kai dauki a fashewa ta farko da ta auku mintoci biyar kafin na biyun a Abuja,, Nigeria, 01 Oktoba 2010

An tsare wani dan Najeriya a Afrika ta Kudu dangane da tagwayen hare haren boma bamai da aka kai ranar jumma’a da suka yi sanadin mutuwar mutane goma sha biyu kusa da inda ake bukukuwan samun ‘yancin kai, a babban birnin tarayyar kasar.

An tsare wani dan Najeriya a Afrika ta Kudu dangane da tagwayen hare haren boma bamai da aka kai ranar jumma’a da suka yi sanadin mutuwar mutane goma sha biyu, kusa da inda ake bukukuwan samun ‘yancin kai, a babban birnin tarayyar kasar. Kakakin rundunar ‘yan sandan ciki ta Najeriya Marilyn Ogar, ta shaidawa manema labarai jiya asabar cewa, ‘yan sanda a Johannesburg, Afrika ta Kudu, suna tsare da wani mutum da ake kira Henry Okah. Okah shine tsohon shugaban kungiyar Movement for the Emancipation of Niger Delta, ko MEND, wadda ta dauki alhakin fashe-fashen. Kungiyar mayakan ta ce an shafe shekaru hamsin ana sacewa mutanen Niger Delta kasa da kuma albarkatunsu. Kungiyar MEND ta yi gargadi dangane da fashe fashen sa’a daya kafin suka auku ranar jumma’a. Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yace wadanda suka kai harin, suna fakewa ne da fafatukar yankin Niger Delta mai arzikin man fetir domin cimma wata manufa ta kashin kansu.