An Tsagaita Wuta Tsakanin Isra'ila Da Falasdinawa

Musayar wuta tsakanin Isira'ila da Falasdinawa

Yanzu haka an tsagaita wuta tsakanin Isira'ila da Falasdinawa, bayan da kasar Masar da wasu kungiyoyi biyu su ka shiga tsakani.

Jami’an Falasdinawa sun ce an cimma tsagaita wuta tare da Isra’ila da kungiyar Hammas da kuma kungiyar Islamic Jihad.

An dai cimma wannan yarjejniyar ce tare da taimakon kasar Masar wadda ta shiga tsakani, wacce za ta fara aiki da misalin karfe 1:30 agogon kasar.

Akwai alamun cewa, ya zuwa yanzu, tsagaita wutar ta fara aiki.

Musayar makaman roka da kuma hare-hare jiragen sama, sun hallaka fararen hula ‘yan kasar Isra’ila guda 4 da kuma Falastinawa akalla 20 tun ranar Juma’a.

Wannan shi ne karon farko da aka kashe Yahudawa fararen hula a fadan na kan iyaka, tun bayan shekarar 2014.

Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta na goyon bayan Isra’il dari-bisa-dari yayin da ta ke kare ‘yan kasarta daga hare-haren rokar Falasdinawa da ake cillowa daga yankin Gaza.