A ci gaba da neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka ‘yan wasan Najeriya Super Eagles sun tashi canjaras da takwarorinsu na kasar Saliyo a karawar da suka yi filin was ana Stevens da ke birnin Freetown a yau Talata.
A karawar da bangarorin biyu suka yi a ranar Juma’ar da ta gabata a birnin Benin, Saliyo ta yi nasarar tafiya da maki bayan da suka tashi kunnen doki 4-4.
Masu fashi baki da dama sun kalli wasan na Freetown a matsayin wanda ya zama jazaman Najeriya ta lashe, amma abin ya cutura.
A wasanta na gaba, Najeriya wacce ta taba lashe kofin gasar har sau uku, za ta kara da kasar Lesotho wacce ta taba dokewa da ci 4-2 a watan Nuwambar 2019.
Bayan da suka buga wasa hudu, ‘yan wansan na Super Eagles na ci gaba da zama a saman teburinsu na “L” da maki 8, sai Benin mai maki 7, Saliyo na da maki 3 yayin da Lesotho ke da maki 2 a kokarin shiga gasar ta AFCON wacce za a yi badi.