An Tarwatsa Shirin Wasu Matasa Na Bukin Casu Maza Da Mata

Wasu rahotanni sun bayyana irin shirye-shirye da wasu matasa ke yi na gabatar da bukin sharholiya,

Wasu gungun matasa da ba'a san ko suwaye ba suna kokarin shirya wani buki mai take 'Yola Beach Party' bukin da iyaye da kuma kungiyoyi ke zargin na nuna tsaraici ne.

Wannan shine karo na biyu da matasan ke shirya irin wannan buki, da kan hada samari da 'yan mata domin holewa, a wannan karon rundunar 'yan sandar jihar Adamawa ta ce ba zata kyale ba.

Kakakin rundunar 'yan sandar jihar ta Adamawa DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce hukumar su ta samu labarin wannan bukin, kuma hakan yasa suka tashi tsaye wajen ganin bukin bai gudana ba, don kuwa sun dau alwashin kawo karshen irin wannan mugunyar dabi'ar a ciki da wajen jihar.

Haka kungiyar 'Adamawa Concern Citizen.' na daya daga cikin kungiyoyin kare hakkin al'umma a jihar, ta bayyana bacin ranta kan wannan batu. Hon Hussaini Gambo Bello Nakura, shugaban kungiyar ya ce basa goyon bayan irin wannan halin na matasa.

Ya kara da cewar hakan babbar matsala ce da ba'a san ina zata kai ba, don kuwa yanzu matasa suke haddasa mafi akasarin matsaloli da ke fuskantar jama'a. Don haka akwai bukatar iyaye su tashi tsaye wajen tarbiyar 'ya'yan su.

Suma wasu iyayeyn sun nuna rashin jin dadin su akan yadda ake samun irin wadannan bata garin da suke shirya irin wadannan sharholiyar.

Ya zuwa yanzu dai wadanda suka shirya bukin, basu bayyanar da kansu ba, ko yin wasu abubuwa da zasu nuna su a bainar jama'a, a bangare daya kuwa jami'an tsaro na cigaba da farautar su.

Ga rahoton Ibrahim Abdul'aziz a cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Tarwatsa Shirin Wasu Matasa Na Bukin Casu Maza Da Mata