Rundunar sojin Najeriya tana cigaba da samun nasara wajan yunkurin murkushe kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram da ke cigaba da kai hare hare a arewa maso gabashin Najeriya.
Rahotanni na nuna cewar a ranar Asabar da ta gabata, sojojin sun yi wani artabu da 'yan kungiyar ta Boko Haram a dajin Sambisa inda sojojin suka bada rahotannin cewar sun hallaka 'yan kungiyar da dama sun kuma kona sansanonin 'yan kungiyar har guda goma da kuma gano makamai da dama wadanda suka hada da motoci masu sulke.
Mai magana da yawun rundunar sojojin Najeriya Kanal S.K Usman yayi karin hasken cewa sojojin Najeriyar sun sami nasarar tarwatsa wani babban sansanin 'yan kungiyar da ake kira Dura Camp wanda aka dauki wasu lokuta ana gumurzu kafin aka sami nasarar hakan.
Kakakin ya cigaba da bada bayanin cewar baya ga wannan babban mazaunin 'yan kungiyar, akwai wasu manyan sansanonin da ke yankin Izza guda hudu da sojojin suka kama kuma sun kone komi da ke wannan sansanin sai dai a cewar shi wani abin takaici guda shine, dakarun sunyi asarar wani soja guda daya yayin da ya taka wani bam da 'yan kungiyar suka binne.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5