“Muna tamkar a wata matalauciyar kasa a duniya kuma abin kunya ne,” in ji Trump ya fada yayin muhawarar da aka watsa ta talabijin ga kasa baki daya, daga hedkwatar gidan talabijin na CNN da ke Atlanta.
“Ba a mutunta mu,” in ji Trump, yana zargin Biden. “Suna tunanin mu wawaye ne.”
Biden ya mayar da martani lokaci guda, yana kallon Trump. Tare da cewa “Wannan shine shugaban kasa mafi muni a tarihin Amurka. Wannan mutumin bai san ma'anar dimokuradiyyar Amurka ba.”
Haduwar Biden-Trump, watanni hudu gabanin zaben ranar 5 ga watan Nuwamba, ita ce muhawara ta farko da aka taba yi a zagaye na hudu na zaben shugaban kasar Amurka.
Hakanan sake haduwa ne tun muhawarar su guda biyu a shekarar 2020, wanda ya faru a cikin watanni biyu kafin Biden ya kayar da yunkurin sake zaben Trump na wa'adi na biyu a Fadar White House.
Muhawarar ta ranar Alhamis ita ce karo na farko da shugabannin Amurka biyu suka taba yin muhawara a tsakaninsu, kuma shi ne karo na farko, da Biden da Trump suka hadu a daki daya tun bayan muhawarar da suka yi a watan Oktoban 2020.
Trump ya tsallake bikin rantsar da Biden a watan Janairun 2021, kuma tun daga lokacin suka yi ta zage-zage da juna, ciki har da matakin muhawara a daren Alhamis.
A cikin 'yan kwanakin nan, Trump ya yi ba a game da shirye-shiryen muhawarar Biden, inda ya ba da shawarar cewa zai bukaci karin karfi daga likita don samun damar iya muhawarar ta mintuna 90, gaba da gaba.
Trump ya fada wa wani gangamin magoya baya a Philadelphia cewa, “A yanzu haka, Joe ya tafi gidan katako don yin nazari,” yayin da yake zayyana alamomi da hannunsa. “Yanzu yana barci, saboda suna son ya sami karfi.”