Ana Kokawa Kan Daukewar Wutar Lantarki A Nijer

Matsalar wutar lantarki a jamhuriyar Nijer

Matsalar wutar lantarki a jamhuriyar Nijer ta haifar da damuwa a wajen al’umma sakamakon lura da yadda a ‘yan kwanakin nan a ke fuskantar daukewar wuta akai-akai  inda a kowace rana akan shafe lokaci mai tsawo ba tare da an sami wutar ba lamarin da ke shafar al’amuran rayuwar yau da kullum.

A yayinda kamfanin wutar lantarki na kasa Nigelec ke cewa tangarda ce aka samu akan layin jigilar wuta na birnin Kebbi ita kuwa jama’a na nuna rashin gamsuwa da wannan hujja.

Ganin yadda kamar da wasa daukewar wutar lantarki ke neman zama Ruwan dare a ‘yan kwanakin nan a nan Nijer musamman a jihohin da ake kira na yankin kogin kwara wato fleuve kokuma kogin Issa wadanda suka hada da Dosso Yamai da Tilabery ya sa jama’a ta fara koka wa kan wannan al’amari da a yanzu haka ake dandana kudarsa kamar yadda za a ji daga bakin wasu mazaunan birnin Yamai.

Matsalar wutar lantarki

A karkashin wata yarjejeniyar kasuwancin da aka cimma a shekarun baya jamhuriyar Nijer na sayen wutar lantarki daga Najeriya sabili kenan kamfanin wuta na Nigelec ke danganta halin da aka shiga da faduwar falwayar jigilar wuta, sai dai labarin ya sha bamban a wajen wasu ‘yan kasa irinsu Salissou Abba mai gareji.

A rubutacciyar sanarwar da ya fitar kamfanin wutar lantarki ya alakanta matsalar da ake fama da ita akan tangardar wayar da aka samu akan hanyar birnin kebbi zuwa Dosso to amma wani kusa a kungiyar kare ‘yancin jama’a a fannin makamashi CODDAE Droit A l’Energie. Abba Dan illela Oummani na cewa bai gamsu da wannan hujja ba . A ra’ayinsa ake bukatar gurfanar da kamfanin wuta na kasa a gaban koliya saboda zargin saba alkawali.

Muryar Amurka ta tuntubi jami’ar hulda da manema labarai a kamfanin Nigelec Mme. Ada Binta ta wayar telehon don jin inda aka kwana game da aiyukan gyaran wannan matsala sai dai ba ta amsa kira ba, haka shi ma ministan makamashi Ibrahim Yacouba da muka kira, bai daga wayar ba.

Jamhuriyar Nijer kasar da Allah ya hore wa hasken rana ya kuma albarkace ta da kogin kwara fleuve Niger na ci gaba da samar da wutar lantarki ta hanyar injina haka a dai dai lokacin da illolin canjin yanayi ke toye aiyukan da galibin ‘yan kasar ke dogaro akansu wato noma da kiwo.

Saurari shirin a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Shiga Matsalar Wuta A Nijer Sanadiyar Faduwar Falwaya A Tsakanin Birnin Kebbi Da Dosso