Ana mataki na karshe na gwajin fasahar network din nan na 5G, mai sauri, wanda aka kwatanta saurin sa akan sau hamsin zuwa dari fiye da wanda ake amfani da shi a yanzu wato 4G.
Wannan sabuwar fasaha zata cigaba da bunkasa harkokin kasuwanci inda ake kyautata zaton daga yanzu zuwa shekara ta 2025, mutane Biliyan 1.2 zasu samu damar amfani da fasahar, a cewar kungiyar fasahar wayoyin hannu da ake kira GSMA.
Ci gaban da aka samu a wannan fasaha zata taimaka wajan saukaka amfani da wayoyin hannu da harkokin kasuwanci na zamani, sai dai hakan ka iya kasancewa babban kalubale ga kasashe da kamfanonin da basu shirya sosai a wannan sabon zango ko kuma sauyi na fasahar 5G, ba.
Ba kamar tsohuwar fasahar 2G da aka samar tun farkon shekarun 1990, ba, ko kuma fasahar 3G, da aka samar tsakanin shekarun 2000, da kuma 4G, zuwa shekarun 2010, ba, fasahar 5G, zata inganta da kara saurin wayoyin hannu da sauran na’urori, da jiragen ruwa da sauran su.