Kamfanin BlackBerry ya kai kamfanin Facebook kara akan manhajar WhasApp da Instaergram, cewar fasahar sa ce kamfanin na facebook ya sata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya wallafa.
Lamarin ya faru ne makonni kadan bayan an zargi shugaban kamfanin Mr John Chen, da boye wa da guzuma yana harbin karsana, wato amfani da faduwar kasuwar da kamfanin keda ita a da domin nemawa kamfanin kudin shiga.
A karar da kamfanin ya shigar a babbar kotun gwamnatin tarayya dake jihar Los Angeles, ta kasar Amurka, kamfanin BlaBerry ya ce wadanda ake tuhumar sun saci fasahar manjahar sa ta aika sakon kar ta kwana.
Kare martabar masu saka hannun jari da ta kamfani na daga cikin rawar da kowane shugaba ya kamata ya taka a cewar mai Magana da yawun kamfanin na BlackBerry, Sarah McKinney, awani sako ta email.
Mataimakin mai bada shawara na kamfanin facebook Paul Grewal, ya bayyana cewa kamfanin a shiye yake domin fuskantar lamari.
Facebook Forum