Duniya ta maida hankali a kan Bahamas, inda dubun dubatan mutane da suke cikin bakin ciki suka fara gwagwarmayar sake gina rayuwarsu biyo bayan barnar da mahaukaciyar guguwar nan ta Dorian.
Rukunin aikin bincike da ceto na kasa da kasa ya baza ma’aikata a fadin tsibiran Abaco da Grand Bahamas domin ceto mutane. Ma’aiakatn sun fara kwashe buraguza a kan hanyoyi domin fara aikin raba kayan abinci da ruwa.
Ma’aikatar tsaro gabar tekun Amurka da sojojin ruwan Birtaniya sun tsaya da jiragen ruwa a tsibiran kana Majalisar Dinkin Duniya tana aikawa da tan tan na abincin da za’a iya ci kai tsaye da kuma na’urorin sadarwa mai amfani da taurarin dan Adam.
Da yammacin jiya Alhamis, adadin mutane da suka mutu a Bahamas ya kai talatin, amma kuma ganin yadda ruwa ya lalata kauyuka da wuraren shakatawa, jamai’ai sun ce akwai yiwuwar adadin zai karu.