An Sauke Kwamandan Rundunar Mayakan Nijar

Yayin da ake jiran ganin yadda za ta kaya a game da wasu dubban miliyoyin CFA da suka yi batan dabo a ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar, shugaban kasar Issouhou Mahamadou ya sallami kwamandan rundunar mayakan kasar Kanal Boulama Issa Zana daga mukaminsa, matakin da ya sake farfado da wata sabuwar mahawara a tsakanin ‘yan kasar.

Taron majalisar ministoci na karshen makon jiya ya bada sanarwar sallamar Kanar Boulama Issa Zana daga mukaminsa na kwamandan rundunar mayakan sama, inda aka maye gurbinsa da mataimakin sa Kanal Amirou Abdoul Kader.

A watannin baya kungiyoyin fararen hula na CCAC suka sanya hukumomin Nijer gaba don ganin an hukunta masu hannu a almundahanar.

Wani jami’an fafutuka Abdou Idi ya ce, sakarwa bangaren shari'a mara ya yi aiki dai dai da abinda doka ta tanada shi ne abinda ake jira daga bangaren zartarwa.

Assoumana Mahamadou dake kare manufofin gwamnatin ta jam'iyyar PNDS ya kara jaddadawa ‘yan kasa aniyar da shugaban ya sa gaba kan batun yaki da cin hanci da rashawa.

Ce-ce-ku-ce a game da kudaden makamai ya samo asali bayan da shugaba Issouhou ya umurci sabon ministan tsaro Firam Issouhou Katambe ya kaddamar da bincike akan matsalolin dake tarnaki a yakin da Nijer ke gobzawa da ‘yan ta’adda, sakamakon mummunar asarar rayukan sojojin da aka fuskanta a karshen shekarar 2019 akan iyakar kasar da Mali.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Shugaban Nijar Ya Tsige Kwamandan Rundunar Mayakan Kasar