Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Da Alamar China Na Wa Afurka Leken Asiri


Hedikwatar Kungiyar Kasashen Afurka (AU) da China ta gina a Habasha.
Hedikwatar Kungiyar Kasashen Afurka (AU) da China ta gina a Habasha.

Wani rahoto na gargadin cewa mai yiwuwa kasar China na amfani da gine-ginen gwamnatocin Afurka da ta gina wajen leken asirin jami’an gwamnatocin kasashen na Afurka.

Rahoton na cibiyar Heritage Foundation, wadda zauren ‘yan ra’ayin rikau ne da ke Amurka, ya gano cewa kamfanonin China sun gina gina gine-ginen gwamnati wajen 186 a Afurka, sannan su suka kafa wasu cibiyoyin sadarwa 14 masu masu matukar muhimmanci. Wadannan gine-ginen sun hada da gidajen Shugabannin kasashe, shugabannin majalisun dokokin kasa da kuma hedikwatocin ‘yan sanda da sojoji.

앙골라 카빈다의 건설현장에서 외국인 노동자들이 일하고 있다. (자료사진)
앙골라 카빈다의 건설현장에서 외국인 노동자들이 일하고 있다. (자료사진)

(Wani muhimmin gini da China ke yi a Angola)

Wanda ya hada hancin rahoton, Joshua Meservey, wanda babban mai nazarin harkokin Afurka ne a cibiyar ta Heritage Foundation, ya ce binciken da aka yi bai samu hujjojin da su ka nuna aka gudanar da harkokin leken asiri a wadannan gine-ginen ba, to amma y ana mai imanin cewa akwai bukatar a kara bincike.

“Gwamnatin China na da dadadden tarihi na duk wani nau’i na leken asiri da sa ido a fadin duniyar nan.” Abin da Meservey ya gaya ma Muryar Amurka kenan ta kafar Skype. “Don haka mu na sane da cewa irin wannan abin ne su ke son yi, abin da kuma su na na sukunin yi din. Sannan kuma Afurka na da matukar muhimmanci gare su ta yadda za su so yin hakan.” A cewar Meservey.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG