An Sanar Da Kafa Gwamnatin Hadin Gwiwa A Congo

A karkashin yarjajjeniyar raba madafun iko, za a bai wa jam’iyyar DC ta su Tshisekedi mukamai 23, a yayin da kuma mukamai 42 za a bai wa mambobin jam’iyyar su tsohon Shugaban kasar, Joseph Kabila, ta CFC.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta ba da sanarwar kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Wannan sanarwar na zuwa ne watanni takwas bayan da Shugaba, Felix Tshisekedi, ya ci zaben Shugaban kasar, wanda aka jinkirta na lokaci mai tsawo.

“A karshe dai an samu gwamnati,” abin da Firaminista, Sylvestre Ilunga Ilukamba, ya fada kenan jiya Litini.

Ya kara da cewa, “Shugaban kasa ya rattaba hannu kan dokar, kuma kwanan nan za mu fara aiki.”