Da misalin karfe 8:30 ne dai jama'ar jihar suka fita kada kuri'unsu, duk da cewa an fuskanci tashin hankali a wasu wuraren jihar. Rundunar tsaron 'yan sandan jihar Edo ta ce ta kama wasu 'yan bangar siyasa dauke da bindigogi.
An dai dauki kwararan matakan tsaro saboda fargabar aukuwar tashin hankali, yayin da 'yan bindiga suka sha alwashin kai hare hare a ranar zaben. A halin da ake ciki, an baza jami'an tsaro a sassan jihar da ke aikin sintiri don tabbatar da zaman lafiya.
Wannan karon dai jama'a basu fita kada kuri'a ba sosai saboda fargabar rashin tsaro, hakazalika an kuma samu tashin hankali a wasu sassan jihar. Rundunar 'yan sandan jihar ta ce ta kama wasu 'yan bangar siyasa dauke da makamai kuma zata gurfanar da su gaban kotu, kamar yadda mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar SP Moses Joel ya bayyana.
Hukumar zabe ta kasa a jihar ta ce an samu tsaiko wajen rarraba kayan aikin zaben saboda rashin isassun jami'an tsaro da zasu raka ma'aikatan zabe. Su ma masu kada kuri'a sun bayyana ra'ayoyinsu.
"Gari yayi shuru, kuma a gaskiya mutane ba su fito kada kuri’a ba sosai,’’ a cewar wata 'yar jihar da ta kada kuri'arta.
Haka shi ma wani mai suna Asue Ighodalo, ya bayyana damuwa kan barazanar tsaro a yayin da ake tsaka da kada kuri'a, a lokacin da ya zanta da manema labarai bayan kada kuri'arsa. Ighodalo ya zargi 'yan sanda da kama 'yan jam'iyyarsa a wata rumfar zabe.
“A rumfar zabe ta Uromi 3, wasu mutane dauke da makamai sun kama daya daga cikin magoya bayanmu, a ka'ida bai kamata wani ya rike makami a rumfar zabe ba, hakan ya saba wa doka, amma duk da haka sai ka ga mutane na abubuwan da ba su kamata ba, suna zaluntar jama'a tare da yunkurin razana mutane," a cewar Ighodalo.
Ya kuma bayyana lamarin a matsayin mai daure kai, kasancewar magoya bayan jam'iyyarsu ne kawai ake kamawa.
''Ta yaya za a ce magoya bayan wata jam’iyya daya ne kawai za a rika kamawa, bayan ga 'yan jam'iyyar da ke mulki na aikata abubuwan da ba su kamata ba?, a cewar Ighodalo.
Shi ma dan takarar gwamna na jam'iyyar APC Monday Okpebholo, ya ce ya yaba da yadda hukumar zabe ta kasa ta ke tafiyar da aikinta, Mr. Okpebholo ya bayyana hakan ne bayan kada kuri'arsa.
Hukumar da ke yaki da almundahana da dukiyar kasa ta EFCC ta ce ta kama wasu 'yan siyasa da ake zargi da hannu wajen raba kudade a yayin zaben na gwamnan jihar Edo.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar:
Your browser doesn’t support HTML5