Shugaban Kwamitin yaki da Polio, kuma mai martaba Sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, yace su na samun ci gaba sosai a wannan kokari
WASHINGTON, DC —
Mai martaba sarkin Dass, Alhaji Usman Bilyaminu Usman, wanda shi ne shugaban kwamitin yaki da cutar Polio a Jihar Bauchi, yace su na ci gaba da samun tazara a kokarin da suke yi na kawar da wannan cuta a jihar.
A cikin wata hirar da yayi da Ibrahim Alfa Ahmed na sashen Hausa, jim kadan a bayan wani taron da hukumar kiwon lafiya tun daga matakin farko ta Jihar Bauchi ta shirya a fadarsa dake garin Dass, mai martaba Usman yace a yanzu, ana samun dafawar shugabannin siyasa da na addini da kuma na al'umma baki daya a cikin wannan yunkurin.
Ya gabatar da misalai da dama na inda aka kwana a wannan yunkurin, kamar yadda zaku ji bayaninsa a cikin wannan hira.

Your browser doesn’t support HTML5