Bisa ga binciken, yawancin wadanda aka yiwa tambayoyi sun bayyana cewa, sun kamu da zazzabin cizon sauro sau daya ko fi a shekarar da ta wuce, sai kuma kashi talatin da hudu bisa dari suka ce basu yi zazzabin ba a cikin watanni goma sha biyu da suka shige.
Binciken ya nuna cewa, wadanda suke zaune a kudancin kasar sun fi wadanda suke arewa kamuwa da zazzabin cizon sauro. Rahoton ya kuma nuna cewa, mata sun fi maza zuwa asibiti domin neman jinyar zazzabin cizon sauro inda kashi arba’in bisa dari suke zuwa asibiti neman magani, kashi talatin da takwas bisa dari kuma suke zuwa su sayi magani a kemis yayinda kashi goma sha uku bisa dari suke amfani da maganin gargajiya kamar shan ganyen dogon yaro ko wadansu ganyaye da ciyayi.
Bincike ya kuma nuna cewa, har yanzu mutane da dama suna tsammani ana iya daukar cutar kanjamau daga cizon sauro.