An Samu Sabani Kan Umurnin Da 'Yan awaren Biafra Suka Bayar

A jihar Imo, an samu rarrabuwar kawuna akan umurnin hana fita a ranar Juma’a, 14 ga wannan watan, wanda kungiyar ‘yan awaren Biafra ta IPOB ta ayyana a duk fadin yankin kudu maso gabas, don nuna fushi akan bacewar madugun kungiyar, Mista Nnamdi Kanu. da kuma iyayensa, wadanda har yanzu, ba’a gano inda suke ba.

Yayin da kungiyar 'yan aware ta masu fafutukar Biafra ta ba da umurnin a zauna a gida a ranar Juma'a domin jawo hankalin hukumomi kan fitar da bayanai game da shugabansu Nnamdi Kanu, an samu rarrabuwar kawuna kan bin wannan umurni a jihar Imo, da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Ni dan Najeriya ne kuma dan asalin kabilar Igbo. A game da ranar 14 ga watan nan da kungiyar IPOB ta hana fita, a gani na ba shi da wani tasiri, saboda zan bude shogona, in kuma gudanar da kasuwanci a ranar. Ba zan dauki ranar a matsayin ranar hana fita ba a kasar Igbo." Inji Mista Ezealor Blessing Henry, mazaunin birnin Owerri.

Ya ce amma idan ka dubi lamarin kungiyar IPOB da bacewar Nnamdi Kanu, gwamnatin tarayya ta san abin da ya fi dacewa ta yi game da ‘yan gwagwarmayar nan da ke yunkurin ficewa.

Mista Ezealor ya ce me yasa gwamnati ba za ta dauki matakan da za su kawo zaman lafiya mai dorewa ba?

Ya kamata shugaban kasa ya dauki mataki, yana mai cewa kashe su ba shi ne abin yi ba wajen magance rikicin kungiyar IPOB.

A cewar shi, "kamata ya yi shugaban kasa ya kirasu kan teburin sulhu su warware rikicin gaba daya.”

A na ta ra’ayin kuma, Amuche Obialor, mai sayar da abinci ta ce, “Ina so a sako Nnamdi Kanu daga duk inda yake. Yana da amfani a gare mu kuma muna bukatar kasar Biafra. Saboda haka, zan kasance a cikin daki a ranar. Ba zan fita ba.”

Tun ranar Litinin, kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar, Malam Dasuki Galadanci ya yi gargadin cewa hukuma za ta cafke duk wanda aka tarar yana karya doka a game da umurnin hana fitan a ranar Juma’an, 14 ga wata.

Ya yi wannan gargadin ne a taron hadin gwiwan da shugabannin hukumomin tsaro a jihar suka gudanar a Owerri, babban birnin jihar, inda ya kara da cewa, daga jiya Talata, hukumomin tsaro za su fara zagaye na nuna iko a sassan jihar, don isarwa ‘yan awaren IPOB sako.

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Rarrabuwar Kawuna A Jihar Imo Kan Umurnin Hana Fita Da IPOB Ta Bada 3'34