Mazauna garin Gurin dake kan iyakar Najeriya da Kamaru sun bayyana cewa takaddamar ta taso ne da jama’an garin suka fito jerin gwano, don nuna fushin su game da matsalar yawaitar garkuwa da jama’a da ake yi domin neman kudin fansa, da kuma tursasawa masu ababen hawa da ake zargin wasu jami’an tsaro ke yi domin karbar cin hanci.
Kuma wannan ya zo ne yayin da aka kafa dokar hana hawa mashin mai kafa biyu a fadin jihar.
Da farko dai sai da mazauna garin suka yi jerin gwano zuwa fadar hakimin garin domin mika kukan su, amma kuma daga baya sai lamarin ya kazance, yadda aka ji daga bakin wasu da al'amarin ya shafa.
Da wakilin Muryar Amurka ya tuntubi kakakin rundunan 'yan sandan jihar Adamawa DSP Suleiman Yahya Nguroje, yace tuni aka tura manyan jami’an tsaro zuwa yankin don gano abun da ya faru.
Gwamnatin jihar Adamawa ta fitar da wata sanarwar gaggawa ta hannun babban sakataren dindindin na ma’aikatar yada labarai Mr Polycarp Ayuba, inda ta bukaci jama’ar yankin da su kwantar da hankulansu za’a dau mataki.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz
Your browser doesn’t support HTML5